Isa ga babban shafi
Wasanni - Ingila

Gasar Firimiya: Iheanacho yayi bajinta, City ta kama hanyar lashe kofin bana

Dan wasan Najeriya dake Leicester City Kelechi Iheanacho, yayi bajinta a ranar Lahadi, bayan jefa kwallaye 3 shi kadai a ragar Sheffield United, a wasan da suka lallasa ta da 5-0.

Kelechi Iheanacho, Dan wasan Najeriya dake Leicester City.
Kelechi Iheanacho, Dan wasan Najeriya dake Leicester City. AP - Rui Vieira
Talla

Nasarar ta Leicester, ta bata damar darewa mataki na biyu na wucin gadi da maki 56, sai dai daga bisani Manchester United ta sake komawa kan matsayi na biyun a gasar ta Firimiya bayan doke West Ham da 1-0 a ranar Lahadi.

'Yan wasan Manchester City yayin murnar kwallon da Sergio Aguero ya jefa, yayin wasa da suka lallasa Fulham da 3-0.
'Yan wasan Manchester City yayin murnar kwallon da Sergio Aguero ya jefa, yayin wasa da suka lallasa Fulham da 3-0. © Reuters

Manchester City ta kara tazarar makin dake tsakaninta da mabiyanta a Firimiyar bayan lallasa Fulham da 3-0 a ranar Asabar, nasarar da ta bata jumilar maki 71, maki 14 tsakaninta United dake biye da ita a matsayi na 2.

Gabriel Jesus, da Sergio Aguero da kuma John Stones ne suka ciwa City kwallayen da suka kara kusantar da ita ga samun nasarar lashe kofin gasar Firimiya na farko cikin shekaru 4.

Dan wasan Tottenham Erik Lamela, yayin kokarin jefa kwallo a ragar Arsenal.
Dan wasan Tottenham Erik Lamela, yayin kokarin jefa kwallo a ragar Arsenal. © Reuters

Ita kuwa Arsenal ta samu nasara kan Tottenham da kwallaye 2-1 ne ta hannun ‘yan wasanta Martin Odegaard da kuma Alexander Lacazette.

Tottenham ce ta soma jefa kwallo a ragar Arsenal ta hannun dan wasan ta Lamela, kafin daga bisani reshe ya juye da mujiya.

A halin yanzu Arsenal na matsayi na 10 da maki 41, yayin da Tottenham ke matsayi na 7 da maki 45. 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.