Karon farko cikin shekaru 18, City ta lallasa Liverpool a Anfield
Manchester City ta lallasa Liverpool da 4-1 yayin fafatawar da suka yi a gasar Premier.
Wallafawa ranar:
Karo na farko kenan cikin shekaru 18 da City ta samu nasarar lallasa Liverpool a filin wasanta na Anfield.
‘Yan wasan City da suka hada da Ilkay Gundogan, Raheem Sterling da Phil Foden, ne suka jefa kwallayen hudu a ragar Liverpool, yayin da Mohammed Salah ya ciwa mai masaukin bakin kwallon ta 1 tilo.
Kayen da Liverpool ta sha a wasan na karshen mako shi ne na uku a kakar wasa ta bana, wanda ya sanya ta cigaba da zama a mataki na 4 a Premier da maki 40, maki 10 kenan tsakaninta da Manchester City dake jagorantar gasar da maki 50.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu