Isa ga babban shafi
Wasanni-Zakarun Turai

Mai yiwuwa Leipzig ta karbi bakuncin Liverpool a Hungary maimakon Jamus

Masu ruwa da tsaki wajen shirya gasar cin kofin zakarun Turai na tattaunawa kan bukatar sauya inda za a fafata wasan zagaye na biyu tsakanin Liverpool da RB Liepzig daga Jamus zuwa birnin Budapest dake kasar Hungary.

Tambarin gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai.
Tambarin gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai. UEFA.com
Talla

Sauya fagen da wasan ya zama dole ne, la’akari da cewar har yanzu dokar hana shige da ficen baki da Jamus ta kafa na cigaba da aiki kan kasashe da dama ciki har da na Turai, domin dakile annobar Korona, musamman sabon nau’in cutar mai saurin yaduwa.

Ranar 16 ga watan Fabarairu aka tsaida domin karawar tsakanin Liverpool da RB Leipzig, kuma hukumar kula da kwallon kafar Turai UEFA tace ya zama dole kungiyar ta Jamus ta nemi yadda za ta karbi bakuncin fafatawar zagayen farko, ko kuma ta fuskanci hukuncin bata rashin nasara a wasan da kwallaye 3-0, kamar yadda dokokin kwallon kafa suka tanadar.

Tuni dai itama takwarar kungiyar ta Leipzig, Burossia Moenchengladbach ta soma nazarin yadda itama za ta bullowa wasan da za ta karbi bakuncin Manchester City ranar 24 ga watan nan na Fabarairu a gasar zakarun nahiyar Turan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.