Coronavirus: Seria A da Premier sun tsaida ranakun kammala hutun dole
Hukumar kwallon kafar Ingila ta bayyana 17 ga watan Yuni a matsayin ranar da za a cigaba da fafata wasannin gasar Premier, bayanda annobar coronavirus ta tilastawa fannin wasanni a duniya tafiya hutun dole.
Wallafawa ranar:
Cikin sanarwar da ta fitar, hukumar shirya wasannin na Premier tace a ranar ta 17 ga watan Yuni, za a fafata tsakanin Aston Villa da Sheffield United, sai kuma Manchester United da Arsenal, yayinda kuma sauran wasannin kasar za su dora daga ranar 19 ga watan na Yuni.
A makwannin baya ranar 1 ga watan Yuni gwamnatin Birtaniya ta bayyana a matsayin lokacin da gasar kwallon kafar Premier za ta cigaba da gudana a kasar, kafin daga bisani a sauya lokacin.
Zuwa yanzu dai sama da mutane dubu 37 annobar coronavirus ta halaka a Birtaniya, daga cikin dubu 269 da 127 da suka kamu ad cutar.
A Italiya kuwa, ministan wasannin kasar Vincenzo Spadafora, yace a ranar 20 ga watan Yuni babbar gasar kwallon kafar kasar ta Seria A za ta cigaba da gudana, bayan shafe watanni uku tana hutun dole saboda cutar coronavirus.
Kawo yanzu cutar ta halaka sama da mutane dubu 33 a kasar, daga cikin dubu 231 da 732 da suka kamu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu