Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Firimiya:Liverpool ta bada tazarar maki 22 a tebur

Liverpool ta kaddamar da gagarumin jagoranci a tarihin gasar Firimiyar Ingila bayan gagarumar nasarar da ta samu a kan Southampton a ranar Asabar.

Jurgen Klopp, kocin Liverpool ta Ingila.
Jurgen Klopp, kocin Liverpool ta Ingila. Phil Noble/Reuters
Talla

Kungiyar ta dare kan teburin gasar ne da tazarar maki 22 tsakaninta da wacce ke ta biyu wato Manchester City bayan lallasa Sothampton 4-0 a filin Anfield.

Kungiyar ta kuma cimma tarihin da City ta kafa na lashe wasanni 20 a jere a gida, abin da tawagar Liverpool ta shekarar 1972 karkashin Bill Shankly ce kawai ta taba shafe tsawon lokaci a gida tana samun jera nasara a wasanni a gasar Firimiya.

Sai dai mai horar da ‘yan wasan Liverpool din Jurgen Klopp ya ce ko kadan bai gamsu da kokarin da suka yi ba inda ya ce tazarar maki 73 ya so su bada.

Kwallaye 4 bayan hutun rabin lokaci da Liverpool ta ci Southampton ne ya ba ta nasarar da yanzu wasanni 42 ta buga a jere ba a doke ta ba, kuma hakan na nufin ta kwashi maki 100 daga 102 da suka rage a gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.