Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Messi na bukatar komawa Real Madrid don ya nuna shi gwarzo ne - Gatti

Tsohon mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Boca Juniors Hugo Gatti, dan kasar Argentina, ya ce dole ne fa shahararren dan kwallon kafar duniya, Lionel Messi ya koma Real Madrid don ya tabbatar da cewa shine dan wasa mafi shahara a tahirin tamaula.

Lionel Messi dan wasa Barcelona da Argentina.
Lionel Messi dan wasa Barcelona da Argentina. Sergio Perez/Reuters
Talla

Tsohon mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Boca Juniors Hugo Gatti, dan kasar Argentina, ya ce dole ne fa shahararren dan kwallon kafar duniya, Lionel Messi ya koma Real Madrid don ya tabbatar da cewa shine dan wasa mafi shahara a tahirin tamaula.

Gatti ya ce Messi, wanda ya kwashe ilahirin lokacinsa na sana’ar kwallon kafa a Barcelona ba zai shiga sahun ‘yan wasa kamar Cristiano Ronaldo, Diego Maradona da Pele ba, sai ya gwada kwanjin sa a wata kungiya ba.

Tsohon mai tsaron ragar ya kuma yi tsokaci kan rashin tabuka abin kirki da Messi ke yi a tawagar kwallon kafar Argentina, yana mai cewa hakan na daga cikin abubuwa da suka rage mai aji.

Messi, wanda yanzu shekarunsa 32 ne ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa ta Ballons d’Or har sau biyar, ya kuma ci 608 sannan ya taimaka aka ci 247 a wasanni da ya buga wa Barcelona a dukkan gasanni, haka kuma a La liga, sau biyar ya lashe kyautar wanda ya fi zura kwallo a raga, ya kuma lashe irin ta sau shida a gasar zakarun nahiyar Turai.

Ya lashe kofuna da dama da kungiyar sa ta Barcelona ciki har da kofin la liga 10, da na zakarun Turai 4, da Copa Del Rey 6.

Sai dai duk da haka, Messi, a tawagar kasar sa Argentina yana shan kashi a duk lokacin da ya kai wasan karshe a gasar kofin duniya da Copa America duk da cin kwallaye 68 tare da taimakawa da ya yi aka ci 44 a wasanni 136 da ya buga wa kasar sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.