Isa ga babban shafi
wasanni

Manchester City casa Huddersfiled

Manchester City ta jefe kwallonta ta 100 a cikin wannan kaka a wasan da ta casa Huddersfield da ci 3-0 a gasar firimiyar Ingila, abin da ya ba ta damar rage tazarar makin da ke tsakanita da Liverpool mai jan ragamar teburi.

Pep Guardiola, da wasu daga cikin 'yan wasansa a  Manchester City
Pep Guardiola, da wasu daga cikin 'yan wasansa a Manchester City Reuters/Paul Childs
Talla

Yanzu haka akwai tazarar maki hudu tsakanin Manchester City da Liverpool wadda ta doke Crystal Palace da ci 4-3 a ranar Asabar.

Leroy Sane ne aka bayyana a matsayin gwarzon dan wasa a fafatawar ta jiya, saboda rawar da ya taka tare da zura kwallaye biyu a ragar Huddersfield wadda ke cikin tsaka mai wuya domin kuwa a yanzu ita ce ta karshe a teburin firimiyar Ingila da maki 11.

Tuni Huddersfield ta shiga neman kwararren kocin din din din da zai cire mata kiste a wuta, in da har ma ta tuntubi kocin Borrusia Dortmund, Jan Siewert .

Ita ma Tottenham ta samu nasarar casa Fulham da kwallaye 2-1a karawarsu ta jiya.

Tuni kocin Fulham Claudio Raneiri ya yi tsokaci kan wannan karawar, in da yake cewa, kungiyar na da karsashinta duk da dukan da Tottenham ta yi ma ta kuma za ta ci gaba da gumurzu.

A bangare guda, Dele Alli  ya samu rauni a karawarsu da Fulham, abin da ya kara ta’azzara matsalar masu fama da rauni a Tottenham wadda ke a matsayi na uku a teburi.

Alli wanda ya ci kwallo daya a karawar ta jiya, ya fice daga filin wasa cikin dingishi a minti na 86.

Baya ga Alli, akwai Hary Kane da shi ma ke fama da raunin da ake ganin zai ci gaba da jinya har zuwa farkon watan Maris, yayin da Moussa Sissoko shi ma zai yi zaman makawanni biyu na jinya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.