Isa ga babban shafi
Wasanni

Bana fargabar makoma ta a Real Madrid - Lopetegui

Kocin Real Madrid Julen Lopetegui, ya ce har yanzu hankalinsa a kwance yake dangane da makomar mukaminsa, duk da matsin lambar da yake sha, a dalilin jerin rashin nasarorin da kungiyar ke fuskanta a karkashinsa.

Sabon mai horar da kungiyar Real Madrid  Julen Lopetegui.
Sabon mai horar da kungiyar Real Madrid Julen Lopetegui. REUTERS/Juan Medina/File Photo
Talla

Lopetegui ya bayyana haka ne a wannan Juma’a, yayinda Real Madrid ke shirin tunkarar wasanta da Levante a wannan Asabar mai zuwa, 20 ga watan Oktoba.

A halin ake ciki, Real Madrid tana kan matsayi na 4 a gasar ta La Liga bayan shan kaye a dukkanin wasanni hudu da ta buga a baya bayan nan ba kuma tare da ta jefa kwallo ko da daya ba.

Karon farko kenan da kungiyar ta fuskanci irin wannan koma baya tun bayan shekara ta 1985.

A baya bayan nan dai, wasu kafafen yada labaran Spain, sun rawaito cewa, akwai yiwuwar Real Madrid ta maye gurbin sabon kocinta Lopetegui da tsohon mai horar da Chelsea Antonio Conte, idan har kungiyar ta ci gaba da fuskantar shan kaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.