Isa ga babban shafi
wasanni

An fitar da Najeriya daga gasar neman kofin duniya

Kasar Argentina ta yi nasarar zuwa zagaye na gaba a gasar neman kofin duniya da ke gudana a Rasha, bayan doke Najeriya ci 2-1 a karar da suka yi birnin Saint Petersburg a yammacin ranar talata.

Dan wasan Najeriya William Troost-Ekong na nadamar kashin da suka sha 2-1 a hannu Argentina ranar 26 ga watan yunin 2018 a St-Petersburg
Dan wasan Najeriya William Troost-Ekong na nadamar kashin da suka sha 2-1 a hannu Argentina ranar 26 ga watan yunin 2018 a St-Petersburg REUTERS/Sergio Perez
Talla

Dan wasan Argentina Lionel Messi ne ya zura kwallon farko a ragar Najeriya a daidai mintuna na 14 da fara wasan, kafin daga bisani dan wasan Super Eagles Victor Moses ya rama wannan ci ta hanyar bugun penariti a minti na 51, wannan dai na nufin cewa an fitar da Najeriya daga gasar ta bana

Keftin na kungiyar kwallon kafar Najeriya Mikel Obi, wanda ke zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala wasan, ya ce ya yi matukar mamaki a game da yadda alkalin wasan ya ki hura pinariti duk da cewa dan wasan Argentina Marcos Rojo ya taba kwallon da hannunsa a mintuna na 76 da fara wasa kuma a daidai farfajiyar kusa da mai tsaron raga.

Lionel Messi, ya ce tabbas Argentina ta yi nasara, amma ba ya tsammanin cewa ya taba buga wa kasar shi wasan da ya ba shi wahala kamar wanda suka buga da Najeirya a ranar ta talata ba.

Ya ce da farko sun kasance a cikin fargaba biyo bayan rashin samun kyakkyawan sakamako a wasanni biyu da suka buga a baya, na biyu kuwa shi ne yadda wasansu da Najeriya ya kasance mai zafi fiye da yadda ake zato.

Mai horas da ‘yan wasan Najeriya Gernot Rohr, ya tabbas ya yi nadma a game da rashin samun nasarar Super Eagles, to sai dai ya ce ‘yan wasan sun taka gagarumar rawa musamman bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci, inda ya ce matukar dai ‘yan wasan Super Eagles suka cigaba da kasancewa a hakan, to lalle Najeriya na da kyakkyawan fata a cikin shekaru 4 masu zuwa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.