Isa ga babban shafi
Wasanni

Maradona zai gana da tawagar Argentina kan wasansu da Super Eagles

Fitaccen dan kwallon Argentina Diego Maradona ya bukaci ganawa da tawagar kwallon kafar kasar gabanin wasansu da Super Eagles ta Najeriya a gobe Talata.

Argentina dai a wasanta na farko ta yi canjaras da Iceland inda a wasa na biyu kuma ta sha kaye da ci 3 da nema a hannun Croatia.
Argentina dai a wasanta na farko ta yi canjaras da Iceland inda a wasa na biyu kuma ta sha kaye da ci 3 da nema a hannun Croatia. Reuters/Muhammad Hamed
Talla

Maradona wanda ya caccaki kamun ludayin ‘yan wasan na Argentina a gasar cin kofin duniyar da ke ci gaba da gudana, ya ce ko ta yaya ne dole Argentinar wadda ta lashe kofin duniya har sau biyu ta yi nasara kan Super Eagles ta Najeriya don kai wa zagayen kasashe 16.

Cikin bacin rai Maradona ya nuna rashin gamsuwarsa da salon shugaban hukumar kwallon kafar ta Argentina Claudio Tapia, inda ya ce abin zai zo da sauki idan da daya daga cikin kasashen Jamus ko Brazil, ko kuma Spain ko Holland ce ta lallasa su sabanin Croatia.

Argentina dai a wasanta na farko ta yi canjaras da Iceland inda a wasa na biyu kuma ta sha kaye da ci 3 da nema a hannun Croatia.

Matukar dai Argentina na son ci gaba da kasancewa a cikin gasar dole ne ta lallasa Najeriya a wasan na gobe, yayinda a bangere guda ita kuma Najeriya ke bukatar ko da canjaras ne don yin waje da Argentinar ko da dai Kociyanta Gernot Rohr ya ce gagarumar nasara ya ke bukata ba canjaras.

A rukunin na D, yanzu Najeriya ce ke matakin na biyu da maki 3 bayan Croatia mai maki 6, yayinda Iceland da Argentina kowanne ke da maki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.