Isa ga babban shafi
wasanni

Babu alaka tsakanin tafiyar Ronaldo da murabus dina- Zidane

Tsohon kociyan Real Madrid Zinadine Zidane wanda ya sanar da murabus dinsa a jiya Alhamis ya musanta cewa saboda wasu manyan ‘yan wasa za su bar Club din ne yasa ya ajje mukamin na sa.

Zidane dai shine Kociyan Real Madrid na farko a tarihi da ya taba ajje aiki a radin kansa ba tare da an kore shi ba.
Zidane dai shine Kociyan Real Madrid na farko a tarihi da ya taba ajje aiki a radin kansa ba tare da an kore shi ba. REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

A wani taron manema labarai Zidane ya ce murabus din nasa bashi da nasaba da kowanne dan wasa kawai dai ya ajje aikin ne a lokacin da yak e ganin shi ne ya dace.

Cikin hanzari Zidane ya amsa tambayar wani dan jarida da ke son sanin ko tafiyar ta sa na da alaka da tafiyar Cristiano Ronaldo? inda Zidan a hanzarce ya ce ko kadan hakan bai da alaka.

Zidane wanda ya kira kansa da mai sa’a amma ba kwararre ba, cikin hujjojin da ya kafa na barin Real Madrid akwai batun cewa ‘yan wasan na bukatar sabuwar murya da za ta horar da su, kuma baya tunanin sa’ar da ya yi ta lashe kofin zakarun turai za ta kara maimaita kanta.

Sai dai duk da haka wasu na ganin ajje aikin na Zidane baya rasa nasaba da yadda Club din ke shirin rasa-jiga-jigan ‘yan wasan har guda 5 ko 6 ciki har da Christiano Ronaldo.

Kusan Ilahirin 'yan wasan sun jimama da rashin Kociyan wanda suka ce tamkar mahaifi ya ke a wurinsu, yayinda mutane da dama ke ganin murabus din nashi na a matsayin babbar koma baya ga kungiyar.

Zidane dai shine Kociyan Real Madrid na farko a tarihi da ya taba ajje aiki a radin kansa ba tare da an kore shi ba, kasancewar Shugaban Club din Florentino Ferez ya yi kaurin suna wajen korar kwaca-kwacai daga bakin aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.