Isa ga babban shafi
wasanni

Zidane ya ajiye aikin horar da Real Madrid

Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya sanar da ajiye aikinsa na horar da kungiyar a wannan Alhamis bayan kwanaki kalilan da jagorantar ta wajen lashe kofin gasar zakarun nahiyar Turai karo na uku a jere.

Zinédine Zidane ya lashe wa Real Madrid kofin zakarun Turai sau uku a jere
Zinédine Zidane ya lashe wa Real Madrid kofin zakarun Turai sau uku a jere REUTERS/Juan Medina
Talla

Zidane mai shekaru 45 ya yanke shawarar ajiye aikin ne a dai dai lokacin da tauraruwarsa ke haskawa, in da ya ce, lokaci ya yi na samar da sauyi a rayuwarsa da kuma Klub din kanta.

Kocin ya kuma ce, ba shi da tabbas game da kwarewarsa ta ci gaba da kafa tarihin samun nasarori a kungiyar ta Real Madrid.

A cewar Zidane, babu wata kungiya da ke da hannu a wannan matakin da ya dauka na raba gari da Real Madrid, amma dai masharhanta na alakanta shi da komawa Faransa don ci gaba da horar da tawagar kwallon kafar kasar.

Sai dai ya ce, a halin yanzu babu wani mukami da yake kwadayin samun sa.

Sanarwar murabus dinsa ta zo da ba-zata kamar yadda shugaban Real Madrid Florentino Perez ya bayyana.

A cikin watan Janairun shekarar 2016 ne, Zindane ya karbi aikin horar da Real Madrid bayan ta sallami Rafael Benitez, yayin da ya lashe ma ta kofuna tara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.