Isa ga babban shafi
Wasanni

"Real na tattare da kakkarfar zalamar lashe kofin zakarun turai"

Yayinda ya rage kwanaki uku a buga wasan karshe na gasar zakarun turai, mai horar da Real Madrid Zinaden Zidane, ya ce ‘yan wasansa na tattare da zalamar son lashe kofin gasar fiye da ko yaushe, duk da cewa sun dauki kofunan gasar sau 3 cikin shekaru 4 da suka gabata.

Mai horar da kungiyar Real Madrid Zinédine Zidane.
Mai horar da kungiyar Real Madrid Zinédine Zidane. AFP PHOTO / GERARD JULIEN
Talla

Madrid dai na neman sake lashe kofin gasar zakarun turan ne karo na uku a jere, yayinda a bangaren Liverpool, karo na farko kenan da ta samu kaiwa ga wasan karshe na gasar tun bayan shekarar 2007.

A cewar Zidane Madrid ba za ta taba canzawa daga dabi’a da kuma alkibllar da aka santa a kai ba, ta neman kari akan kari, duk da dinbin nasarorin lashe kofuna da ta samu a baya.

Wasu dai na kallon wasan karshen da za a fafata a Kiev da cewa za a tantance gwarzo ne tsakanin Cristiano Ronaldo da Muhammad Salah na Liverpool.

Sai dai a lokacin da manema labarai suka tambayi Zidane ko zai iya bada Ronaldo ya karbi Salah a matsayin musaya, babu kai kawo kocin yace ‘a’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.