Isa ga babban shafi
Wasanni

‘Likitoci ne zasu tabbatar da tsawon lokacin da Pogba zai shafe yana jiyya’

Mai horar da kungiyar Manchester United Jose Mourinho, ya musanta rahotanni da ke cewa dan wasansa na tsakiya Paul Pogba, zai shafe makwanni masu yawa ba tare da ya sake buga wasa ba, sakamakon raunin da ya samu, a lokacin wasan da suka lallasa kungiyar Basle, da kwallaye 3-0 a Gasar Cin Kofin Zakarun Nahiyar Turai.

Mai horar da kungiyar Manchester United Jose Mourinho.
Mai horar da kungiyar Manchester United Jose Mourinho. Reuters/Jason Cairnduff
Talla

Rahotannin sun ce Pogba wanda fice daga filin wasan yana dingishi zai shafe akalla makwanni 12 ba ba tare da sake shiga fili ba, sakamakon raunin.

Sai dai a martaninsa, Mourinho ya ce babu gaskiya cikin rahotannin da ake yadawa, ba kuma za’a tantance gaskiyar tsawon lokacin da Pogba zai shafe yana jiyya ba, har sai likitoci sun fitar da sakamakon binciken da suka yi, dan haka zai iya zama kwanaki 12 kawai dan wasan zai yi ko kuma sama da haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.