Isa ga babban shafi
Wasanni

Barcelona ta kulla kwamtiragi da Paulinho

Kungiuyar kwallon kafa ta Barcelona ta cimma yarjejeniyar kulla kwantiragi da dan wasan Brazil kuma tsohon dan wasan tsakiya a Tottenham, wato Paulinho daga kungiyar Guanghzou ta China.

Dan wasan Brazil Paulinho da ya kulla kwantiragi da Barcelona
Dan wasan Brazil Paulinho da ya kulla kwantiragi da Barcelona Reuters/Andres Stapff
Talla

Barcelona ta kulla kwantiragin ne akan farashin Euro miliyan 40, kuma a karon farko kenan da kungiyar ta siyo wani dan wasa tun bayan da ta raba gari da Neymar de Silva Santos, wanda ya koma Paris St Germaine akan farashin Euro miliyan 222.

A ranar Alhamis mai zuwa ne ake saran Paulinho mai shekaru 29 zai yi gwajin lafiyarsa a Spain.

Dan wasan dai ya nema wa kansa wuri na din-din a tawagar kwallon kafar Brazil tun bayan da kasar ta dauko Tite a bara don horar da tawagar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.