Isa ga babban shafi
Spain

Tsoffin ‘Yan wasan Barcelona za su fafata da na Manchester United

Tsoffin zaratan ‘yan wasan Barcelona da na Manchester United da za su fafata a  wasan sada zumunci a yau Juma’a a Camp Nou kafin su sake haduwa a Old Traford a watan Satumba.

Za a yi karawar ne misalin karfe 7 na dare agogon Najeriya
Za a yi karawar ne misalin karfe 7 na dare agogon Najeriya FC Barcelona
Talla

Tawagar tsoffin ‘Yan wasan Barcelona ta kunshi Ronaldinho da Rivaldo da Patrick Kluivart da Edger David da Edmilson.

Tawagar Manchester United kuma za ta kunshi yawancin ‘yan wasan da suka lashewa kungiyar gasar cin kofin zakarun Turai a 1999 da suka hada da Paul Scholes da Phile Neville da Ji Sung-Park da Luis Saha da Edwin van der Sar.

An shirya wasan ne dai da nufin samar da kudi ga asibitin cutar Kansa ta Barcelona da ke kula da yara kanana.

Tsoffin ‘Yan wasan Barcelona za su kai wa Manchester ziyara a ranar 2 ga watan Satumba domin sake samar da gidauniyar kudi ga cibiyar Manchester United.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.