Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Ronaldo ya fi Messi samun kudi a bana

Cristiano Ronaldo ya zarce Lionel Messi a matsayin dan wasan da ya fi samun kudi mafi tsoka a kwallon kafa a kakar 2016 zuwa 2017, kamar yadda binciken Mujallar Faransa ta kwallon kafa ya tabbatar.

Cristianno Ronaldo dan wasan Real Madrid
Cristianno Ronaldo dan wasan Real Madrid REUTERS/Ruben Sprich
Talla

A yau Talata Mujallar Faransa da ke tsokaci kan kwallon kafa ta wallafa rahoton cewa Ronaldo na karbar kudi miliyan 87.5 na yuro, yayin da Messi ke samun kudi yuro miliyan 76.5.

Mujallar ta ce Bincikenta ya shafi albashi da kudaden lada da kuma kudaden tallace tallace da ‘yan wasan na kwallon kafa ke samu.

Neymar ne na uku da kudi miliyan 55.5 na yuro. Sai Gareth Bale a matsayi na hudu da kudi yuro miliyan 41.

Mujallar kuma ta ce Jose Mourinho na Manchester United ne kocin da ya fi karbar kudi a duniya inda ya ke karbar yuro miliyan 28.

Ronaldo dai ya doke Messi a gasar kyautar gwarzon dan wasan duniya ta Ballon d'Or da mujallar Faransa ke bayarwa da kuma kyautar FIFA a bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.