A Gabon za a yi gasar Afrika duk da tarzoma- CAF
Hukumar kwallon kafar Afrika CAF ta ce za a yi wasannin gasar cin kofin Nahiyar a Gabon duk da kasar ta fada cikin rikicin siyasa bayan sake zaben shugaba Ali Bongo.
Wallafawa ranar:
CAF ta ce ba wani sauyi kuma za ta ci gaba da shirye shiryen karbar bakuncin gasar.
Gabon dai za ta dauki nauyin wasannin ne a tsakanin 14 ga watan Janairu zuwa 5 Fabrairu.
A Libya ya kamata a gudanar da gasar amma saboda rikicin da ake yi a kasar aka janye aka ba Gabon.
CAF ta ce shirin hada kasashen da za su kara a rukunin farko na nan kamar yadda aka tsara a ranar 19 ga watan Oktoba a birnin Libreville.
Sai dai kakakin hukumar Junior Binyam ya ce ana iya samun sauyi amma hakan ya dogara ne da sakamakon babban taron da CAF za ta gudanar Al Kahira a ranar 21 ga watan Satumba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu