Isa ga babban shafi
Barcelona

Haraji: Barcelona za ta tsaya wa Messi

Barcelona ta ce zata tsaya wa Messi bayan zartar masa da hukuncin dauri kan kaucewa biyan haraji. Kungiyar ta kaddamar da kamfen na nuna goyon baya ga dan wasanta a shafukan sadarwa na Intanet.

Ana zargin Messi da Mahaifin shi kan kaucewa biyan haraji a Spain
Ana zargin Messi da Mahaifin shi kan kaucewa biyan haraji a Spain REUTERS
Talla

Barcelona ta kirkiro da shafi #WeAreAllMessi wato dukkanmu Messi ne, tare da wallafa hoto da ke dauke da sako zuwa ga magoya bayan kungiyar su fito su bayyana goyon bayansu akan Dan wasan.

Sanarwar da ta fito daga shugaban kungiyar Josep Maria Bartomeu ta ce masu adawa da Messi na adawa ne da Barcelona, don haka kungiyar za ta ci gaba da yaki akan Dan wasanta har sai ya yi nasara.

Kotun Sifaniya dai ta zartar da hukuncin daurin watanni 21 akan Messi kan laifin kaucewa biyan haraji tare da cin dan wasan tarar kudi sama da euro miliyan 2 da shi da mahaifin shi.

Sai dai tuni Messi ya daukaka kara a kotun kolin Spain.

A tsarin dokar Spain dai akwai yiyuwar za a dakatar da hukuncin saboda bai kai shekaru biyu ba kuma kasancewarsa laifin farko ne wanda bai shafi rikici ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.