Isa ga babban shafi
Wasanni

Fifa ta tuna da marigayi Yekini na Najeriya

Wallafawa ranar:

A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Intanet, hukumar FIFA ta tuna da kwallon da Yekini ya jefa a ragar kasar Bulgaria a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a Amurka a shekara ta 1994.Wannan kwallon dai, ita ce ta farko da Najeriya ta ci a gasar cin kofin duniya, yayin da Yekini ya shiga cikin ragar yana girgizata, yana kuka domin nuna farin cikinsa na zura wannan kwallo mai cike da tarihi.Ya dai rasu a ranar 4 ga watan mayun shekarar 2012 bayan ya yi fama da rashin lafiya. Sannan ya bar duniya yana da shekaru 48 da haihuwa.Ramatu Garba Baba ta yo mana dubi a kai tareda kawo wasu labaren wasanni a cikin shirin Duniyar Wasanni. 

Rashidi Yekini lokacin a cikin ragar Bulgeria bayan zira kwallon shi ta farko a gasar cin kofin Duniya da aka gudanar a kasar Amurka a shekarar 1994
Rashidi Yekini lokacin a cikin ragar Bulgeria bayan zira kwallon shi ta farko a gasar cin kofin Duniya da aka gudanar a kasar Amurka a shekarar 1994 Nigerian Vanguard
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.