Isa ga babban shafi
Wasanni

Platini ya soki kwamitin FIFA

Shugaban hukmar kwallon kafa ta nahiyar Turai da aka dakatar, Michel Platini ya yi kakkausar suka ga kwamitin daukaka kara na hukumar kwallon kafa ta duniya bayan kwamitin ya goyi bayan hukuncin da aka dauka a kansa na dakatar da shi daga shiga harkokin wasanni.

Michel Platini
Michel Platini AFP
Talla

A jiya Laraba ne, hukumomin FIFA suka rage wa Platini da Sepp Blater hukuncin haramcin shiga harkokin wasanni daga shekaru takwas zuwa shida amma duk da haka Platini bai gamsu ba yayin da ya ce, wannan hukuncin na a matsayin cin fuska da tauye hakki.

An dakatar da shugabannin ne guda biyu bayan an zarge su da hannu a badakalar cin hanci da rashawa da ta addabi FIFA, lamarin da ya sa aka haramta wa Platini tsayawa takarar shugabancin hukumar a zaben da za a gudanar a gobe Jumma'a.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.