Isa ga babban shafi
FIFA-U17

U17 : Golden Eaglets sun sake lashe kofin duniya

Najeriya ta lashe kofin duniya na ‘yan kasa da shekaru 17, bayan ‘Yan wasan Golden Eaglets sun doke Mali ci 2 da 0 a wasan karshe a gasar da aka gudanar a jiya Lahadi a kasar Chile.

Najeriya ta kasance kasa ta biyu a tarihin gasar bayan Brazil da ta kare kofin gasar cin kofin duniya na ‘yan kasa da shekaru 17.
Najeriya ta kasance kasa ta biyu a tarihin gasar bayan Brazil da ta kare kofin gasar cin kofin duniya na ‘yan kasa da shekaru 17. Fifa.com
Talla

Victor Osinhen ne ya fara jefa kwallo a ragar Mali, kwallon shi ta 10 a gasar, yayin da kuma Funsho Bamgboye ya jefa kwallo ta biyu. Najeriya ta barar da fanariti ana soma wasan.

Najeriya dai ta kasance kasa ta biyu a tarihin gasar bayan Brazil da ta kare kofin gasar cin kofin duniya na ‘yan kasa da shekaru 17.

Kafin wasan karshe, ‘Yan wasan Najeriya sun casa Brazil ci 3 da 0 a zagayen kwata fainal bayan sun lallasa Australia ci 6 da 0. Kuma Tun a tashin farko suka ba Chile kashi5 da 1.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.