Isa ga babban shafi
Wasanni

Manyan cinikin ‘yan wasa 8 mafi tsada a bana

Kevin De Bruyne ya kasance dan wasa Ma fi tsada da aka yi cinikinsa a bana, bayan Manchester City ta kulla kwantiragi da shi daga Wolfsburg kan £55m.

Facebook @Pich Maxisda
Talla

Raheem Sterling ya kasance na 2 mafi tsada da Manchester City ta yi cinikinsa daga Liverpool kan £49m.

Sai Christian Benteke dan wasa na uku a yanzu mafi tsada da aka yi cinikinsa bayan Liverpool ta kula kwantiragi da shi daga Aston Villa kan £32.5m.

Nicolas Otamendi na Valencia wanda shi ne na 4 a, inda Manchester City ta yo Cefanesa kan £32m.

Na 5 shine Memphis Depay na PSV da yanzu haka ya koma Manchester United kan £31m.

Roberto Firmino wanda ke matakin na 6 Liverpool ta kulla yarjejniyar da shi kan £29m bayan dauko shi daga Hoffenheim.

Na 7 shine Morgan Schneiderlin daga Southampton da ya koma Manchester United kan £25m.

Sai kuma Rodriguez Pedro na 8 mafi tsada da Chelsea ta Sayo shi daga Barcelona kan £21m .
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.