Beijing
Kenya ta samu yawan lambobin yabo a Beijing
Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya jinjinawa ‘Yan wasan kasar kan rawar da suka taka na lashe yawan lambobin yabo a wasannin guje guje da tsalle tsalle na duniya da aka kammala a Beijing.
Wallafawa ranar:
Talla
Wannan ne karon farko da Kenya ta zo a matsayi na farko da yawan lambobin yabo inda ta lashe guda 16 da suka hada da zinariya 7.
Kenya ta sha gaban Jamaica da ta zo a matsayi na biyu da kuma Amurka a matsayi na uku.
Kenya dai ta samu nasarar ne a tseren gudu mai nisan zango.
Birtaniya ce ta zo a matsayi na hudu sai kuma Habasha daga Afrika a matsayi na biyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu