Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Zidane ya kammala karatun shi na Diploma

Tsohon dan wasan kwallon kafan Faransa Zinedine Zidane, da a halin yanzu ke aiki a matsayin mataikin kocin kungiyar Real Madrid, ya kammala karatun diploma da yake yi kan harkokin kula da sha’anin wasanni. Ya yi karatun ne a wata cibiyar koyon shari’a da tattalin wasanni, ta birnbin Limoges, da ke yammacin kasar Faransa.Zidane bai cewa kowa komai game da karatun nashi ba, amma wani da suka yi wasa a kungiyar kwallon kafan Faransa, mai suna Olivier Dacourt ne ya sanya hoton su biyun, a shafin shi na Twitter, cikin hoton, an ga dukkan su dauke da kwalin shedar diplomar tasu, inda ya kuma ce yanzu kam sun kammala karatu.Zidane ya buga wa kungiyoyin Cannes, Bordeaux da kuma Juventus wasa, kafin ya koma Real Madrid a sheakarar 2001, ya kuma yi ritaya daga kwallon kafa a shekarar 2006, lokacin yada da sheakaru 34. 

Tsohon dan wasan kasar Faransa, Zinedine Zidane
Tsohon dan wasan kasar Faransa, Zinedine Zidane ikimedia Commons
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.