Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Everton ta doke Man United a gida,yayin da PSG ta sha kashi a hannu Evian

A gasar Premier ta kasar Ingila, a cikin daren jiya an buga wasanni har guda 9, to sai dai ko shakka babu daga cikin wasanni akwai wadanda suka fi daukar hankulan jama’a da kuma wadanda sakamakonsu ya fi bayar da mamaki.

Darron Gibson dan wasan  Everton
Darron Gibson dan wasan Everton Everton.com
Talla

Misali kararwa da aka yi tsakanin Man United da Everton, Man united ta sha kashi ne ci daya mai ban haushi, kuma abinda ya sa wannan ya fi bayar da haushi, an yi wasan ne a gidan Man United.

Ita kuwa Arsenal ta doke Hull ne ci biyu da nema.
Sai Liverpool da doke Norwich ci 5 da 1
Ashton Villa ta lallasa Southampton ci 3-2
Sai Stoke wadda ta yi canjaras da Cardiff ba wanda ya zura kwallo a ragar wani.

To kamar yadda na fada tun da farko, wasanni guda 9 ne aka buga cikin daren jiya a gasar ta Premier, saboda haka ga yadda sakamakon sauran wasannin ya kasance.

Sunderland ta sha kashi a hannun Chelsea ci 4-3
Swansea kuwa ta doke Newcaslte ne ci 3 da nema.
Fullham kuwa ta sha kashi ne a hannun Tottenham 2-1, yayin da Man City ta tarar da West Brom har gida ta doke ta ci 3 da 2.

 

To bayan nasarar da ta sama a daren jiya, har yanzu dai Arsenal ce ke kan teburin gasar da maki 34, Chelsea na a matsayin ta biyu da maki 30, sai Man City a matsayin ta 3 da maki 27.

To A gasar Ligue 1 ta Fransa ma a cikin daren jiya an buga wasanni har guda 6,
Paris Saint Germain mai rike da kofin kasar Faransa, ta sha kashi a hannun Evian Thonon Gaillard ci 2-0

Sai Ajaccio da ta yi canjaras da Bastia ci daya kowannensu, sai dai an buga wannan wasa ne ba tare da ‘yan kallo ba, sakamakon matakin da hukumar kwallon kafa ta kasar ta dauko domin ladabtar da Club din da magoya bayansa suka taba tayar fitina a filin kwallo,

Monpelier kuwa ta sha kashi ne a hannun Lorient ci 2 da nema, yayin da Rennes ta doke St Etienne ci 3 da 1.

To sai dai duk da wannan kashi da ta sha, har yanzu PSG ita ce kan teburin gasar Ligue 1 da maki 37, sai Lille a matsayin ta biyu da maki 36 yayin da Monaco ke biye masu da maki 35.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.