Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Tsohon dan wasan Super Eagles, Thompson Oliha ya rasu

Tsohon dan wasan Super Eagles na Najeriya Thompson Oliha ya rasu jiya bayan ya yanke jiki a ban daki inda aka garazaya da shi wani asibiti dake Ilorin a Jihar Kwara.

Tsohon dan wasan Super Eagles, Marigayi Thompson Oliha
Tsohon dan wasan Super Eagles, Marigayi Thompson Oliha
Talla

Likitan asibitin Industrial Medicare, Yussuf Abdulrahman ya bayyanawa manema labarai cewa a lokacin da iyalin Oliha suka isa da shi asibiti ya riga ya cika.

Dan wasan ya rasu ne yana dan shekaru 44 yana kuma cikin ‘yan wasa Super Eagles da suka lashe kofin gasar Nahiyar Afrika a shekarar 1994 a Tunisia, kana ya halarci gasar cin kofin Duniya a Amurka.

Izuwa rasuwar shi,Thompson Oliha shike rike da mukamin mai horar da ‘yan wasa a makarantar kwallon kafa ta Jihar Kwara, inda a ranar Asabar din da ta gabata ya jagorancin ‘yan wasan da suka lallasa ‘yan wasan Mali da ci 3-0

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.