Isa ga babban shafi
Tennis

An fidda Andy Murray daga gasar Paris Masters

A cigaba da wasannin Paris Masters, Pole Jerzy Janowicz, ya doke Andy Murray dan kasar Ingila a gasar, bayan sun buga wasanni zagaye uku, inda ya lallasa da ci 5-7, 6-2 da kuma ci 6-2. Murray dai shine dan wasan Tennis na uku a duniya bayan Roger Federer da Novak Djokovic , a yayin da shi kuwa Pole Jerzy shine na 69 a duniya.  

Andy Murray
Andy Murray Reuters/Charles Platiau
Talla

A dai jiya ne aka fidda Novak Djokovic shima daga gasar bayan Sam Querrey dan kasar Amurka ya doke shi.

Wannan ce babbar nasara da Pole Jerzy, dan shekaru 21 ya taba samu, inda aka ganshi ya fadi kasa yana murna bayan ya fidda Murray a gasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.