Isa ga babban shafi
Tennis

Djokovic da Sharapova sun lashe wasanninsu a Wimbledon

Novak Djokovic zakaran Tennis na duniya ya lashe wasan shi na farko a gasar Wimbledon da ake gudanarwa a Birtaniya inda yak e kokarin kare kambun shi, sai dai a Venus Williams ta Amurka ta fice gasar a karawar farko.

Maria Sharapova 'Yar wasan Tennis ta kasar Rasha
Maria Sharapova 'Yar wasan Tennis ta kasar Rasha Reuters/Nir Elias
Talla

Novak Djokovic ya doke Juan Carlos Ferrero ne dan kasar Spain a ranar farko da aka bude gasar Wimbledon a jiya Litinin.
Djokovic shi ne mai rike da kofin gasar bayan ya doke Rafeal Nadal a bara

Venus Williams ta amurka kuma tasha kashi ne hannun Elena Vesnina ‘Yar kasar Rasha.

Jarumar Tennis kuma ta Duniya Maria Sharapova ta tsallake zuwa zageye na biyu bayan ta doke Anastasia ‘Yar kasar Australia a ranar farko ta Wimbledon.

Wannan ne dai wasa na Farko da sharapova ta buga tun lokacin da ta lashe kofin gasar French Open ta Roland Garros a Faransa bayan ta doke Sara Errani ta Italia.

A zagayen na gaba Sharapova zata kara ne tsakaninta da Pironkova ‘Yar kasar Bulgaria.

A yau Talata ne Rafael Nadal wanda ya taba lashe gasar sau biyu zai fara haskawa a Wimbledon, haka ma Petra Kvitova mai rike da kofin a yau Talata zata fara haskawa.

Nadal wanda ya lashe kofin Roland Garros sau Bakwai a yau zai kara ne da Thomaz Bellucci na Brazil.

Andy Murray kuma na Birtaniya zai kara ne da Nikolay Davydenko na kasar Rasha.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.