Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Cristiano Ronaldo yace a Madrid zai yi ritaya

Cristiano Ronaldo yace ba zai bar Real Madrid ba tsawon rayuwar shi. Dan wasan ya fadi haka ne a wata Hira da ya yi da Jaridar Wasanni ta Marca a Spain bayan ya lashe kofin La liga na Farko bana.

Cristiano Ronaldo Dan wasan Real Madrid
Cristiano Ronaldo Dan wasan Real Madrid REUTERS/Juan Medina
Talla

“Zan yi Ritaya a Real Madrid” inji Christiano wanda ya fara taka kwallo a shekarar 2009 da Real Madrid bayan ya baro Manchester United.

Ronaldo yace akwai yiyuwar zai kwashe tsawon shekaru 10 da Karin wasu sama a Benabeur. Domin a cewarsa Rayuwar shi na tafiya dai dai a Spain.

A bana dai Ranaldo yana fatar lashe kyautar kwarzon dan wasan Duniya karo na biyu bayan ya lashe kyautar a lokacin da yana Manchester United. Sai dai an kwashe shekaru uku Lionel Messi yana haramtawa dan wasan kyautar. Kuma ko a bana akwai yiyuwar Messi zai iya lashe kyautar idan har Ronaldo bai yi komi ba a Euro da Olympics.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.