Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

An sallami Muamba daga Asibiti, za’a ci gaba da Seria A bayan mutuwar Morosini

Hukumar kwallon kafa a Italia tace a ranar 25 ga watan Afrilu ne za’a buga wasannin da aka dage saboda mutuwar Morosini dan wasan kungiyar Liverno wanda ya dauke sheda a filin wasa. Fabrice Muamba kuma dan wasan Bolton an sallame shi daga Asibiti.

Dan kasar Congo Fabrice Muamba mai taka kwallo a kungiyar Bolton a Ingila
Dan kasar Congo Fabrice Muamba mai taka kwallo a kungiyar Bolton a Ingila Clive Brunskill/Getty Images
Talla

Likitoci a kasar Italia sun ce sun kwashe sa’o’I Shida ba tare da gano abin da ya yi sanadiyar mutuwar Morosini wanda ya fadi a filin wasa bayan zuciyar shi ta daina harbawa.

Kungiyar Liverno kuma tace babu wani dan wasa da zai sake sa rigar Morosini lamba 25 domin ta sadaukar da lamba gare shi.

Dan wasan Bolton Wonderers, Fabrice Muamba an sallame shi daga Asibiti a jiya Litinin, bayan dan wasan ya samu sauki daga ciwon da ya shafi Zuciya da har yasa dan wasan ya fadi a filin wasa.

Likitici sun ce Mumba sai da ya dauke sheda na tsawon mintina fiye 70.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.