Zambia zata buga wasan karshe tare da tuna ‘yan wasanta da suka mutu
Kasar Zambia zata buga wasan karshe a gasar cin kofin Afrika da kasar Cote d’Ivoire tare da tuna tsuffin ‘yan wasanta da suka mutu a wani hadarin jirgin sama a Gabon a shekarar 1993. A Malabo kuma a gobe Assabar Ghana da Mali zasu Fafata domin neman matsayi na uku.
Wallafawa ranar:
Bayan zuwansu birnin Libreville ne inda zasu kara da Cote d’Ivoire, ‘Yan wasan Copper bullet suka kai ziyara wurin da jirgin sama ya yi hadari da daukacin ‘yan wasan kasar, a lokacin da suke kan hanyarsu zuwa buga wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da Senegal a birnin Dakar.
mutane 30 ne a cikin jirgin, ‘Yan wasa 25 da matuka 5 dukkaninsu suka mutu. A lokacin dai dan wasan Zambia daya ne hadarin bai rutsa da shi ba, waton Kalusha wanda shi ne gwarzon dan wasan Afrika a Lokacin wanda ke taka leda a kasar Holland kungiyar PSV Eindhoven, kuma shugaban hukumar kwallon kafar kasar na yanzu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu