Gabon da E/Guinea sun zama ‘yan kallo a gasar Cin kofin Afrika
kasar Ghana da Mali da Cote d’Ivoire da Zambia sun tsallake zuwa wasan kusa `da karshe. Mali da Cote d’Ivoire ne suka sallami masu daukar nauyi gasar Gabon da Equatorial Guinea a wasan quarter final.
Wallafawa ranar:
A ranar Assabar ne kasar Cote d’IVoire ta doke Equatorial Guinea ci 3-0.
A jiya Lahadi ne kasar Mali ta doke Gabon a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan kammala mintinan wasan ana kunnen doki ci 1-1. Didier Drogba wanda ya zira kwallaye biyu a wasan Cote divoire da Equatorial Guinea yana a babban birnin kasar Gabon lokacin da aka fitar da kasar a gasar.
‘Yan wasan Black Stars na Ghana sun doke Tunisia ne ci 2-1 duk da cewa alkalin wasa ya ba d an wasan Ghana Jan kati.
Yanzu haka a ranar Laraba kasar Ghana zata fafata da Zambia wacce ta doke kasar Sudan a wasan Quarter final.
Cote d’Ivoire kuma zata kara ne da kasar Mali.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu