Isa ga babban shafi

Majalisar Faransa ta amince da dokar zubar da ciki

‘Yan Majalisar Dattawan Faransa, sun kada kuri’ar amincewa da sanya ‘yancin zubar da ciki a kundin tsarin mulkin kasar.Majalisar ta yi zama na musamman ne a ranara Laraba domin tafka muhawara kan duba lamarin.

Wani asibiti a kasar India
Wani asibiti a kasar India AFP/Indian Navy/Handout
Talla

Idan an amince da kudirin da kuri'a kashi uku cikin biyar na 'yan majalisar dokokin kasar, da ake sa rai ranar Litinin, Faransa za ta zama kasa ta farko a duniya da ta tabbatar da 'yancin zubar da ciki a tsarin mulkin kasar.

Sanatocin Faransa sun halarci muhawarar kada kuri'a kan shirin gwamnati na sanya 'yancin zubar da ciki a cikin kundin tsarin mulkin kasar a birnin Paris a ranar 28 ga Fabrairu, 2024.

Kuri'ar ta ranar Laraba ta zo ne bayan da majalisar wakilan kasar, ta amince da kudurin da gagarumin rinjaye a watan Janairu.

Gwamnatin shugaba Emmanuel Macron ta bukaci a yi mata kwaskwarima a sashi na 34 na kundin tsarin mulkin kasar domin yin nuni da 'yancin mata na samun damar zubar da ciki.

Gwamnatin ta ce gabatar da kudirin dokar ya zama dole bayan sake dawo da hakkin zubar da ciki a Amurka, inda a shekara ta 2022 kotun kolin ta soke hukuncin da aka yanke a shekara ta 1973, wanda ya ba da damar yin amfani da tsarin a duk fadin kasar.

Babu daya daga cikin manyan jam'iyyun siyasa da ke da wakilci a majalisar dokokin Faransa da ya nuna shakku kan 'yancin zubar da ciki, wanda aka yi wa kaca-kaca da shi a shekarar 1975. Yawancin Sanatoci sun goyi bayan sauya kundin tsarin mulkin kasar, ko da yake wasu 'yan mazan jiya sun soki lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.