Isa ga babban shafi

Hungary ta sake hana EU baiwa Ukraine tallafin kudi, sa'o'i kadan bayan hana ta shiga kungiyar

Hungary ta dakatar da yunkurin kungiyar tarayyar turai na tallafawa Ukraine da kudade da yawan su ya kai Yuro biliyan 50, sa’o’I kadan bayan da ta hana yunkurin shigar Ukraine din kungiyar tarayyar turai.

Prime ministan Hungary Victor Orban
Prime ministan Hungary Victor Orban REUTERS/Stoyan Nenov
Talla

Hungary ta yi amfani da karfin da take da shi wajen darewa kujerar naki kan dukkan bukatun da aka zo da su don cikawa Ukraine burin ta.

Ko da yake jawabi Prime ministan kasar Victor Orban ya ce a yanzu babu wannan magana ta baiwa Ukraine wadannan kudade ko kuma bata damar shiga EU.

Sai dai kuma duk da haka jagororin kungiyar sun ce za’a sake zama kan wannan batu cikin watan janairu mai kamawa don ganin ko za’a iya shawo kan Hungary.

Ukraine ta dogara ne kachokan kan tarayyar turai da Amurka wajen samun kudade da makaman da take amfani da su wajen ci gaba da kare kanta daga kutsen Rasha.

Ana dai ganin Hungary na zamarwa Ukraine tarnaki ne sakamakon kyakyawar alakar da ke tsakanin ta da Rasha.

Bayanai sun ce Mr Orban bai bata lokaci a dakin taron ba, bayan da ya bayyana matsayar kasar sa na hana Ukraine wadannan kudade ya fice, inda ya bar sauran jami’an kungiyar da karin bayani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.