Isa ga babban shafi

Harin 'yan bindiga ya kashe mutane fiye da 20 a Amurka

Akalla mutane 22 sun mutu sakamakon harin da wasu ‘yan bindiga suka kai birnin Lewiston Maine na Amurka cikin daren jiya kamar yadda jami’an tsaro suka tabbatar, inda suka ce tuni maharan suka tsere.

Ana yawan samun rahotannin 'yan bindiga da budewa jama'a wuta a Amurka a baya-bayan nan
Ana yawan samun rahotannin 'yan bindiga da budewa jama'a wuta a Amurka a baya-bayan nan © AFP
Talla

Bayanai sun ce bayan mutane fiye da 20 din da suka mutu wasu da dama sun jikkata a sakamakon harin.

Magajin garin Robert McCarthy ya shaidawa manema labarai cewa mutane 22 ba wai sun mutu a take bane, wasu sun mutu bayan an kai su abibiti, abinda ke nufin adadin mamatan ka iya karuwa.

Harin ya faru a wani wajen taruwar jama’a mai cike da guraren cin abinci da dakunan san barasa.

Bayanai sun ce jami’an tsaro da masu bayar da agaji sun dauki lokacin kafin isa wajen, abinda ya baiwa maharan damar guduwa

Tuni dai rundunar yan sandan yankin ta wallafa hoton guda daga cikin maharan dauke da wata bindiga mai sarrafa kanta, lokacin da ya budewa wuta kan mai uwa da wabi.

Tuni kuma rundunar ‘yan sandan jihar ta ayyana maharin a matsayin dan ta’adda da ke da matukar hadari, la’akari da samfurin bindigar da yayi amfani da ita.

Har yanzu dai babu cikakken bayani kan inda maharan suke a halin yanzu don haka jami’an tsaro ke rokon jama’a da su sanar da su da zarar sun ganshi ko kuma samun wani bayani gama da inda suke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.