Isa ga babban shafi

Rasha na sha'awar komawa kwamitin kare hakkin dan adam na MDD

Rasha na duba yiwuwar sake mikawa majalisar dinkin duniya bukatar komawa cikin kwamitin kare hakkin dan adam, bayan da aka cire ta a sakamakon afkawa Ukraine.

Shugaban Rasha Vladmir Putin
Shugaban Rasha Vladmir Putin via REUTERS - SPUTNIK
Talla

Tuni dai kasashen duniya suka fara hararar wannan sabon yunkuri na Rasha, wadda a yanzu ake yi mata kallon jagorar kasashe masu fatali da hakkin dan adam.

Za dai a gudanar da kada kuri’ar zaben kasashe 15 da zasu kasance mambobin kwamitin kare hakkin dan adam din na shekarun 2024-2026 nan ba da jimawa ba.

Bisa ala’ada dai ana zaben kasashen ne ta la’akari da nahiyar da suka fito da kuma irin rawar da suka taka wajen kare hakkin dan adam, mutunta dokokin kasa da kasa da kuma tabbatar zaman lafiya.

Wannan bukata ta Rasha na zuwa ne yan sa’o’i bayan harin da ta kaiwa Ukraine da ya kashe mutane 50 a kauyen Groza.

Tuni sashen tsaron sirri na Amurka ya ce kasar na fatan majalisar dinkin duniya zata yi watsi da wannan bukata ta Rasha ba tare da bata wata dama ba.

A baya-bayan nan dai shugabar hukumar kare hakkin dan Adam ta majalisar dinkin duniya Mariana Katzarova, ta ce cin zarafin dan adam da zaluncin da Rasha ke yi a Ukraine ya kai kololuwar da aka jima ba’a ga irin sa ba.

Kafin samun damar komawa cikin kwamitin, Rasha na bukatar kuri’ar kasashe 97 cikin guda 193 mambobin majalisar dinkin duniya.

A watan Afrilun 2022, kasashe 93 suka kada kuri’ar korar Rasha  aga cikin kwamitin, abinda kasar ta yi watsi da shi ba tare da bata lokaci ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.