Isa ga babban shafi

Isra'ila ta yi gargadin shiga yakin da za'a jima ba'a kawo karshen sa ba da Hamas

Gwamnatin Isra'ila da sha alwashi mayar da mumunan martani kan mayakan Hamas na Falasdinawa, bayan harin da suka kaiwa kasar ba ba'a taba ganin mai munin sa ba shekaru 50 da suka gabata.

Prime ministan Isra'ila Benjamin Natenyahu
Prime ministan Isra'ila Benjamin Natenyahu REUTERS - REMO CASILLI
Talla

Bayanai sun ce harin ya hallaka akalla mutane 200 kawo yanzu, kuma akwai yiwuwar adadin ka iya karuwa.

Kamfanin dilancin labaran Faransa AFP ya ruwaito cewa birnin TelAviv ya kasance shiru, a sakamakon munanar da harin yayi.

Bayanai na cewa rabon da kasar ta ga hari mai munin wannan tun shekaru 50 da suka gabata a lokacin yakin Yom Kippur.

Tuni dai TelAviv din ta mayar da martanin harin wanda ya kashe mutane fiye da 230, yayin da Prime ministan kasar Benjamin Natenyahu ke cewa tabbas harin da aka kaiwa kasar sa bude kofar yakin da za’a dade ba’a rufeta bane.

Benjamin Natenyahu ya ce wannan hari tamkar dai tayar da kurar da take barci ne, don haka Hamas ta shirya ganin jerin hare-hare mafiya muni cikin wadanda ta gani a baya, yana mai gargadin nan kusa zai yi wuya a sami wanda zai iya kwantar da wannan tarzoma da ta taso.

Ko a safiyar yau Lahadi, bayanai sun nuna yadda aka gudanar da wata mummunar musayar wuta a tsakanin dakarun Hezboullah da na Isra'ila, a kokarin da kowanne bangare ke yi na mayar da martani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.