Isa ga babban shafi

Jami'an kwastam a Faransa sun kama kokon kan birrai sama da 400 da ake shirin tafiya da su Amurka

Jami’an hukumar hana fasa kwauri ta Faransa sun kama wasu mutane da kokon kawunan birrai fiye da 400, ana shirin kai su kasar Amurka.

Akwai sassan jikin dabbobi da dama da aka haramta shiga ko fita da su daga kasar
Akwai sassan jikin dabbobi da dama da aka haramta shiga ko fita da su daga kasar Getty Images - Pablo Jeffs Munizaga - Fototrekk
Talla

Bayanai sun nuna cewa kokon kawunan birran da aka kama na cikin irin nau’in birran da aka hana kashewa.

Rundunar kwastam din ta cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce ko a watan Disambar bara sai da ta kama kokon kawunan birran da aka haramta kashewa har guda 392 da aka shigar da su kasar ana kuma yunkurin fitar da su zuwa Amurka.

Haka kuma rundunar ta kama kasusuwan wasu dabbobin na daban fiye da guda 100, kuma dukkan su babu amincewar hukumomi a safarar su.

Birran da aka haramta kashewa
Birran da aka haramta kashewa © Getty Images/Anup Shah

Shugaban hukumar kwastam na kasar Gilbert Beltran ya shaidawa manema labarai cewa akwai wasu sassan jikin dabbobi da aka haramta shiga ko fita da su daga kasar, da suka hadar da hauren giwa, da kahon wasu dabbobi da sauran sannan jikin dabbobi masu barzanar karewa.

Gwamnatin kasar ta ce kasusuwan dabbobin da ta kama darajar su ta kai yuro biliyan 20.

Ana zargin haramtattun kungiyoyin sarrafa sassan jikin dabbobi ne zasu yi amfani da wadanan kokunan kan na birrai da za’a shigar da su Amurka ta haramtaciyyar hanya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.