Isa ga babban shafi

Matashin Amurka zai shafe shekaru 22 a gidan yari saboda harin Capitol

Wata Kotu a Amurka ta yanke wa tsohon shugaban wata kungiyar matasa masu tsatsauran ra’ayi hukuncin daurin shekaru 22 a gidan yari, a sakamakon kama shi da laifin taka muhimmiyar rawar a harin ranar 6 ga watan Janairun 2021 da aka kai ginin Capitol na Amurka.

Jagoran matasan da suka kaddamar da hari kan ginin Capitol na Amurka
Jagoran matasan da suka kaddamar da hari kan ginin Capitol na Amurka AP - Allison Dinner
Talla

A yayin yanke hukuncin mai shari’a Timothy Kelly ya ce matashin Enrique Tarrio ya wulakanta Amurka ta hanyar cin zarafin guda daga cikin gine-ginen da suka dauka a matsayin masu dimbin tarihi.

A cewar alkali Kelly, Tarrio na cikin na gaba-gaba wajen shirya matasa da kuma kitsa musu yadda zasu afkawa ginin da kuma lalata kayan da ke cikin sa, da sunan goyon bayan wani dan siyasa.

Tun farko dai tawagar masu shigar da kara na Amurka sun bukaci kotun ya yankewa matashin daurin shekaru 33 a gidan yari, amma la’akari da cewa matashin baya Amurka lokacin da aka aiwatar da laifin, sai kotun ta rage shekaru 11 cikin shekarun da suka bukata.

Bayanai sun ce matashin mai shekaru 39 baya Amurka, a ranar da aka aikata laifin amma kuma shi ne ya hada kan matasa da kuma kitsa musu yadda zasu aikata laifin a matsayin sa na jagoran su.

Baya ga Matashin Enrique an kuma yankewa wani yaron sa mai suna Ethan Nordean hukuncin daurin shekaru 18 a gidan yari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.