Isa ga babban shafi

Kotun New Zealand ta yanke wa uwar da ta kashe 'ya'yanta hukuncin rai da rai

Wata kotu a New Zealand ta kama wata uwa da laifin kashe ‘ya’yanta, inda kuma ta yanke mata hukuncin daurin rai da rai kan kowanne kisa.

Kotun New Zealand ta daure matar da ta kashe 'ya'yanta ba-gaira-babu-dalili.
Kotun New Zealand ta daure matar da ta kashe 'ya'yanta ba-gaira-babu-dalili. © Alexander Nemenov / AFP
Talla

Lauren Anne Dickason yar asalin Afrika ta Kudu ta kashe ‘yan’yanta mata tagwaye ‘yan shekaru biyu, sai kuma yar uwarsu mai shekaru 6, tun a watan Satumbar 2021 a gidan da ke yankin Timaru na New Zealand.

Alkalan da suka saurari karar da suka hada da mata 8 da maza 4 sun amince cewa lokacin da matar ta aikata wannan danyen aiki tana cikin hankalinta kuma ba ta cikin maye.

Tun farko, mai gidanta Mista Graham ne ya fara kai rahoto a ofishin ‘yan sanda bayan da ya ci karo da gawarwakin ‘ya’yansa da kuma matar kwance cikin jini lokacin da ya koma gida daga wajen taron liyafar cin abinci da abokansa.

Bayan gudanar da bincike ne kuma aka kama matar, sai dai har zuwa lokacin da aka yanke mata hukunci ba ta bayar da wani gamsashen dalilinta na aikata kisan ba, kasancewarta mai cikakken hankali kuma ba ta  da wata lalurar kwakwalwa ko kuma matsin rayuwa.

Bayanai sun ce, an kwantar da uwargida Dickason a asibitin masu fama da tabin hankali don karbar gwaje-gwajen likitoci, kafin aka yanke mata hukuncin daurin rai-da rai bayan da rahoton likitoci ya nuna bata da wani tabin kwakwalwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.