Isa ga babban shafi

Soja na karshe cikin dakarun da suka kare Faransa yayin mamayar Nazi ya mutu

Soja na karshe cikin dakarun Faransa da suka baiwa kasar kariya yayin mamayar ‘yan Nazi a 1994 Leon Gautier ya mutu a jiya litinin ya na da shekaru 100 a Duniya. 

Kwamandan dakarun Faransa da suka baiwa kasar kariya yayin mamayar ‘yan Nazi a 1994 Leon Gautier.
Kwamandan dakarun Faransa da suka baiwa kasar kariya yayin mamayar ‘yan Nazi a 1994 Leon Gautier. AP - Ludovic Marin
Talla

Tun da yammacin jiya litinin mahukuntan Faransa suka sanar da mutuwar kwamanda Leon Gautier zakakurin Soji daya tilo da ya yi saura a sahun dakarun kasar da suka kawo karshen mamayar Nazi a yammacin Turai. 

Gautier guda ne cikin Sojojin Faransa 177 wadanda suka Jaa daaga tare mayar da martani ga Sojojin Nazi ranar 6 ga watan Yunin 1944 wanda daga nan ne aka faro nasarar dakile mamayar ta ‘yan Nazi a yammacin Turai 

Duk da yadda Gwamnatin Faransa a wancan lokaci ta mika wuya ga Jamus a 1940, Gautier na sahun sojojin da suka shiga runduna ta musamman da aka yiwa suna Kieffer wadda ta hadu da taimakon Sojojin Amurka da Birtaniya da sauran sojojin kasashen Turai wajen fatattakar Nazi har bayan 1944. 

Magajin garin Ouistreham Roman Bail ne ya sanar da mutuwar Gautier a asibitin Caen yankin gabar teku da dakarun na Faransa a wancan lokaci suka yada zango don shiryawa fafatawa da Sojojin Nazi, kuma yankin ne kwamandan Sojin ya zabi zama don kammala rayuwarsa. 

Babban hafson sojin ruwan Faransa, Admiral Vandier ya wallafa sakon jinjinawa ga Leon Gautier wanda ya ce ya sadaukar da tsawon rayuwarsa wajen hidimtawa kasar lura da yadda ya shiga aikin Soji tun ya na dan shekaru 17 ya kuma bayar da gudunmawa iya karfinsa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.