Isa ga babban shafi

Iyalai a Birtaniya sun shiga damuwa saboda karancin kwai a sassan kasar

Yayin da kasar Birtaniya ke ci gaba da fuskantar kalubalen matsalar tattalin arziki, rahotanni sun ce yanzu haka kasar ta fada matsalar karancin kwai, abinda ya shafi gidaje da dama da suka saba kalace.

Alkaluma sun nuna yadda farashin kwan ya yi tashin gwauron zabi a sassan Birtaniya.
Alkaluma sun nuna yadda farashin kwan ya yi tashin gwauron zabi a sassan Birtaniya. REUTERS/Edgard Garrido
Talla

Bisa al’ada 'yan kasar Birtaniya na sarrafa kwai ta hanyoyi da dama wajen yin kalace, abinda ke bayyana cewar rashin kwan na matukar gibi ga kalacen jama’a.

Tuni wannan karanci ya sa babban kamfanin sayar da kayan masarufin kasar na ‘Asda da Lidl‘ ya fara kayyade adadin kwan da jama’a ya dace su saya.

Wani mai shagon sayar da kayan kalace a tsakiyar Birnin London, Gursel Kirik ya ce kwandon kwan da ya saba saye Fam 20 mai dauke da kwai 360 a ciki watanni da suka gabata, yanzu haka ya tashi zuwa Fam 68, abinda ke barazana ga harkokin kasuwancin su.

Kirik ya ce bashi da tabbacin cewar zai ci gaba da gudanar da harkokinsa nan da watanni 6 masu zuwa saboda hauhawan farashi da kuma tsadar rayuwa lura da yadda farashin makamashi yayi tasho goran zabbi.

Wasu masana tattalin arziki na danganta matsalar karancin kwan da cutar murar tsintsayen da aka samu a kasar da kuma yadda jama’a da dama suka koma amfani da kwan saboda tsadar nama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.