Isa ga babban shafi

Rasha za ta yi amfani da iyakar Belarus don karfafa farmaki a Kiev- Zelensky

Ukraine ta yi gargadi kan yiwuwar fuskantar barazanar hare-hare daga Belarus bayan Minsk da Moscow sun sanar da kulla wata yarjejeniyar bayar da tsaron iyaka a tsakaninsu cikin makon jiya.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky yayin jawabi kan barazanar hadakar Rasha da Belarus.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky yayin jawabi kan barazanar hadakar Rasha da Belarus. AP
Talla

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce Rasha na son yin amfani da salon kulla yarjejeniyar bayar da tsaro ga iyakar Belarus ne don ci gaba da kai farmaki sassan Kiev inda ya sake kira ga kasashen yammacin Duniya kan su kara kaimi wajen ladabtar da Moscow da kuma wadata Ukraine da makamai na zamani.

Gargadin na Zelensky na zuwa a dai dai lokacin da shugana Joe Biden na Amurka ke zargin Iran da taimakawa Rasha wajen girke jami’anta na musamman wadanda ke sarrafa jirage marasa matukan da ke ci gaba da kai farmaki sassan Ukraine.

A cewar Biden ko shakka babu jami’an Iran na zaune yanzu haka a yankin Crimea kuma daga can ne suke sarrafa jirage marasa matukan da Iran ta baiwa Rasha wanda dasu ne Putin ke amfani wajen kai hare-haren baya-bayan nan.

Jiragen marasa matuki samfurin Iran da ake kira “kamikaze” Turai da Amurka na ganin da su ne Rasha ke amfani wajen ci gaba da kai munanan hare-hare sassan Ukraine, lamarin da ya janyowa Tehran karin takunkumai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.