Isa ga babban shafi

Yajin aikin ma'aikatan sufuri ya gurgunta lamurra a Faransa

Faransawa sun fuskanci cikas wajen gudanar da ayyukan yau da kullum a ranar Talata, bayan da kungiyoyin kwadago suka kira yajin aikin sufuri a fadin kasar, sakamakon gaza cimma matsayar kawo karshen yajin aikin da ya gurgunta ayyukan wuraren ajiyar main a defo defo, matakin da ya haifar da karancin man na fetur.

'Yan kwadago sun sha alwashin cigaba da yajin aiki a Faransa.
'Yan kwadago sun sha alwashin cigaba da yajin aiki a Faransa. REUTERS - PASCAL ROSSIGNOL
Talla

Yajin aikin dai na zuwa ne bayan da ma'aikatan matatun mai da ma'aikatun da ke karkashin babban kamfanin makamashi na TotalEnergies suka kada kuri'ar tsawaita yajin aikin da suka shiga.

Yajin aikin ya haifar da cikas ga aikin rarraba mai a duk faɗin kasar musamman a arewaci da tsakiyar Faransa da kuma yankin Paris.

A makon da ya gabata, gwamnatin shugaba Emmanuel Macron ta yi amfani da karfin ikon tilastawa wasu masu zanga-zangar komawa bude rumbunan ajiyar man fetur, matakin da ya harzuka kungiyoyin kwadago, said ai tuni kotu ta goyi bayan matakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.