Isa ga babban shafi

EU ta sake lafta takunkumai kan Rasha da zai shafi man da ta ke fitarwa

Kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da sake kakaba wasu kunshin takunkuman karya tattalin arziki kan Rasha dangane da abin da ta ke aikatawa a Ukraine, cikin takunkuman har da wanda ya kayyade farashin mai da kuma hana fitar da kayayyakin da Moscow ke yi na kusan yuro biliyan bakwai.

Majalisar gudanarwar Turai.
Majalisar gudanarwar Turai. AP - Jean-Francois Badias
Talla

Shugabar hukumar gudanarwar EU Ursula von der Leyen ta ce takunmuman sun kuma kunshi hana wasu da ke taimakawa Rasha tafiye-tafiye da kuma kama wasu kaddarorin su.

Kunshin takunkuman sun kuma haramtawa turawa zama mamba a kwamitocin gudanarwar kamfanoni mallakar gwamnatin Rasha.

Shima jami'in kula da harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai Josep Borrell, ya ce mutanen da wannan takunkumi ya shafa sun hada da wadanda ke taimakawa Moscow wajen kaucewa takunkumin da aka sanya mata.

Tun a watan Mayun da ya gabata, kungiyar ta EU ta amince da haramta shigar da mafi yawan man Rasha zuwa nahiyar.

Yunkurin kara farashin man da EU ta yi, na nufin kayyade yawan kudaden da kasashe irin su China da India ke biya na danyen man Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.