Isa ga babban shafi

Rasha za ta dauki sabbin Soji dubu 300 bayan kashe mata dakaru kusan 6000 a Ukraine

Ma’aikatar Tsaron Rasha ta sanar da kisan sojojinta kusan dubu 6 a yakin da ta shafe tsawon watanni 7 ta na gwabzawa a Ukraine, wanda ke matsayin karon farko da Moscow ke fitar da jumullar alkaluman dakarun da ta yi asara a yakin.

Ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu yayin jawabi kan shirin daukar sabbin Soji dubu 300 da kuma kisan dakarun kasar kusan dubu 6 da ke yaki a Ukraine.
Ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu yayin jawabi kan shirin daukar sabbin Soji dubu 300 da kuma kisan dakarun kasar kusan dubu 6 da ke yaki a Ukraine. AP
Talla

Ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu a wani jawabin kai tsaye da ya gabatar ta gidan talabijin yau laraba, ya ce dakarun kasar dubu 5 da 937 suka mutu a Ukraine tun bayan farowar yakin a watan Fabarairu zuwa yanzu, yakin da Moscow ke nanata cewa ta na yi ne don kare martabar al'ummarta.

Wannan sanarwa na zuwa a dai dai lokacin da shugaba Vladimir Putin ke bayyana wani sabon shirin daukar sabbin sojoji dubu 300 aiki a sassan Rasha, a wani yunkuri da kasashen Duniya ke ganin jagoran na Moscow na shirin karfafa dakarunsa don dorawa a yakin da ya ke a Ukraine, dai dai lokacin da yankin 'yan aware na Ukraine ke shirin kada kuri'ar ballewa daga kasar don hadewa da Rasha.

Tuni dai kasashen Duniya suka fara kakkausar suka ga matakin na Putin, inda kungiyar tarayyar Turai ke ganin yunkurin daukar sojojin dubu 300 ya nuna karara yadda Putin ya damu da rashin nasararsa a yakin na Ukraine, yayinda Jamus ta bayyana yunkurin a matsayin wani lamari da bazai haifarwa kasar da mai ido ba.

A bangare guda jagoran adawar Rasha da ke fuskantar dauri Alexei Navalny ya bayyana cewa matakin daukar sabbin sojojin dubu 300 zai kasance mafi munin kuskure da kasar za ta tafka.

Sai dai yayinda kasashen Duniya suka yi caa kan Putin, shugaba Xi Jinping na China ya bukaci sasanta rikicin kasashen biyu ta hanyar tattaunawa maimakon ci gaba da yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.