Isa ga babban shafi

Jagoran tsohuwar tarayyar Soviet Mikhail Gorbachev ya rasu ya na da shekaru 91

Mikhail Gorbachev, wanda ya kafa sabon tarihi a duniya ta hanyar zama silar rugujewar Tarayyar Soviet, wanda kuma shi ne shugaban tsohuwar makekekiyar kasar na karshe, ya rasu a birnin Moscow yana da shekaru 91.

Jagoran tsohuwar Tarayyar Soviet, Mikhaïl Gorbatchev
Jagoran tsohuwar Tarayyar Soviet, Mikhaïl Gorbatchev AP - Boris Yurchenko
Talla

Kafafofin yada labarai a Rasha sun ce Gorbachev ya mutu ne a wani babban asibiti da ke birnin Moscow a jiya Talata, bayan fama da rashin lafiya mai tsanani, tsawon lokaci.

Gorbachev, wanda ya mulki tsohuwar Tarayyar Soviet tsakanin shekarun 1985 zuwa 1991, ya taimaka wajen rage tsamin dangantakar da ke tsakaninsu da Amurka, shi ne shugaba na karshe a zamanin yakin cacar baka.

Rayuwar Goberchev ta kasance daya daga cikin mafi tasiri a zamaninsa, wanda sauye-sauyen da ya yi a matsayin shugaban Soviet ya ya bai wa yankin gabashin Turai damar ‘yantar da kansu daga karkashin mulkin tsohuwar Tarayyar ta Soviet.

Sauyin da marigayin ya aiwatar ya janyo masa jinjina da ban girma a kasahen yammacin duniya, tare da lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel a shekara ta 1990, sai dai kuma ya zama abin kyama ga ‘yan Rasha da dama wadanda suka yi tir da yadda ya kawo karshen wanzuwar kasarsu a matsayin mafi karfin karfin fada aji a duniya.

Goberchev dai ya shafe fiye da shekaru ashirin da suka gabata ya na kauracewa harkokin siyasa, inda ya rika kira ga Kremlin da fadar White House da su gyara alakarsu, yayin da dangantakar kasashen ke sake tabarbarewa zuwa matakin yakin cacar baka, bayan da Rasha ta mamaye Crimea a shekarar 2014 tare da kaddamar da farmaki a Ukraine a farkon wannan shekarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.