Isa ga babban shafi

Kasashen Turai na cikin shirin-ko-ta-kwana saboda wutar daji

Birtaniya da Faransa na cikin shirin ko-ta-kwana sakamakon tsananin zafi da ya haifar da ibtila’in wutar daji a kasashen kudancin Turai.

Masana kimiya sun ce, dumamar yanayi ne ta haddasa gobarar.
Masana kimiya sun ce, dumamar yanayi ne ta haddasa gobarar. AP
Talla

Masu hasashen yanayi a Birtaniya sun yi gargadi kan irin barnar da zafin ka iya haifarwa a kasar wadda ba ta kinsta  tunkarar yanayin na zafi ba da ya jefa rayukan mutane cikin hatsari.

A can birnin London, an yi hasashen cewa, ma’aunin zafi a cikin dare zai haura maki 38 na Celsius a yau Litinin, yayin da ake sa ran a gobe Talata, makin ya kai 40 a karon farko a tarihin kasar.

Masana kimiya sun ce, matsalar sauyin yanayi ne ta haddasa tsananin zafin da kuma wutar dajin.

Bayanai na cewa, jami’an kwana-kwana sun gaza shawo kan gagarumar wutar da ta yi barna bayan ta tashi a wurare biyu da ke kudu maso yammacin Faransa, yayin da jami’an kashe gobarar suka dauki tsawon kwanaki 6 suna yayyafin ruwa daga jirgin sama domin kashe wutar.

Wutar dajin da ke ci gaba da ruruwa a kasashen Faransa da Girka da Portugal da kuma Spian, ta lalata dubban kadada tare da tilasta wa dubban mutane kaurace wa gidajensu.

Ana dai ci gaba da kwashe dubban mutane yanzu haka daga gidanjesu a yankin kudu maso yammacin Faransa saboda yadda wutar ta ki ci-ta-ki cinyewa.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.