Isa ga babban shafi

EU ta sanya gas da nukiliya a jerin makamashi marasa gurbata muhalli

Majalisar Tarayyar Turai ta amince da kudirin kungiyar EU a ranar Laraba na bayar da damar zuba jari a fannin makamashin iskar gas da na nukiliya, ta hanyar ayyana su a matsayin wadanda basu da hatsarin kara matsalar dumamar yanayi.

Sashen makamashin Nukiliya na Faransa.
Sashen makamashin Nukiliya na Faransa. AP - Bob Edme
Talla

'Yan majalisar Tarayyar Turai 328 suka amince da kudirin, wanda Faransa da Jamus ke marawa baya, yayinda 278 suka hau kujerar naki, sai kuma wasu 33 da suka kaurace, a birnin Strasbourg da ke gabashin Faransa

Gabanin kada kuri’ar da aka yi kan kudurin da ya amince da zuba hannun jari wajen bunkasa fannin samarwa da kuma amfani da makamashin iskar gas da kuma nukiliya  sai da Firaministan Jamhuriyar Czech Petr Fiala, wanda kasarsa ta karbi ragamar shugabancin Tarayyar Turai daga Faransa, ya roki da a yi watsi da batun.

Wadanda ke sukar wannan mataki dai sun bayar da misali da yakin da ake yi a Ukraine a matsayin dalili na baya-bayan da ya kamata a yi amfani da shi wajen kin amincewa da karfafa zuba jari kan amfani da makamashin iskar gas, matakin da suka ce zai sanya a kara dogaro ne akan gas din da Rasha ke samarwa.

Dangane da nukiliya kuwa, masu sukar makamashin sun bayyana barazana da kuma hatsarin dake tattare da shi ne, tare da bayyana cewar amfani da makamashin hasken rana shi ne cigaba mafi kyau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.